Shugaban Majalisar Dattawa ya bukaci shugaba Buhari da ya mikawa majalisun kasarnan wani kudiri na gyara dokar masana’antar mai

0 22

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan a jiya ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mikawa majalisun kasarnan wani kudiri na gyara dokar masana’antar mai.

Ahmad Lawan ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa kafin karanta bukatar shugaban kasar na gyara dokar kasafin kudi ta bana ga kwamitin kasafin kudi bayan da kudirin ya tsallake karatu na biyu.

Ya ce bukatar neman gyara ga dokar masana’antar man fetur za ta baiwa majalisun kasar damar tsawaita tsarin bayar da tallafin mai a dokar masana’antar man fetur.

Wannan, a cewarsa, zai kasance daidai da bukatar shugaban kasa na karin kudi naira tiriliyan 2 da biliyan 557 domin biyan tallafin man fetur a kasafin kudin 2022 daga watan Yuli na wannan shekara.

Ana sa ran tsarin tallafin mai na yanzu zai kare a watan Yuni 2022, bisa tanadin dokar masana’antar man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: