Shugabannin majalisar wakilai za su gana da shugaban kasa Buhari kan yajin aikin da ASUU ke yi

0 71

A gobe talata shugabannin majalisar wakilai za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yajin aikin da mambobin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ke yi.

Wata majiya mai karfi daga fadar shugaban kasa, da ta nemi a sakaya sunanta gayawa manema labarai a jiya, cewa ‘yan majalisar sun shirya mika wa Buhari shawarwarin nasu daga ganawar da suka yi da masu ruwa da tsaki kan yajin aikin.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce majalisar za ta shirya rahoton tsoma bakin majalisar kan yajin aikin da ake yi, kuma za ta gana da shugaban kasa kan lamarin.

Da yake jawabi a taron karshe na shugabannin majalisar da masu ruwa da tsaki da suka hada da mambobin kungiyar ASUU da wakilan gwamnatin tarayya, dan majalisar ya ce rahoton zai yi nuni da yadda suke mu’amala da kungiyar ASUU da kuma bayar da shawarwari domin baiwa shugaban kasa damar tantance halin da ake ciki.

Sai dai Gbajabiamila bai bayyana lokacin da tawagarsa za ta gana da shugaban kasar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: