Hukumar NDLEA ta kai samame wani gidan alfarma a unguwar Lekki a Legas inda ta ce ta gano miyagun ƙwayoyi

0 68

Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa wato NDLEA ta kai samame wani gidan alfarma a Unguwar Lekki a Legas inda ta ce ta gano miyagun ƙwayoyi.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter inda ya ce an gano ƙwayoyin Tramadol guda miliyan 13 a gidan.

Ya bayyana cewa duka ƙwayoyin suna nauyin miligram 225.

Mista Femi ya bayyana cewa gidan babu wani bil adama da ke zaune a ciki, sai dai waɗannan ƙwayoyi da aka ajiye a ciki.

Ya kuma ce tuni aka kama wanda ake zargi da ajiye ƙwayoyin inda a halin yanzu yake hannun NDLEA.

A ƴan kwanakin nan dai hukumar ta NDLEA na wawan kamu inda ko a kwanakin baya sai da ta kama hodar ibilis ta biliyoyin naira da kuma dubban kwalaben A-Kurkura da tabar wiwi a samame daban-daban da ta kai a fadin kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: