Shugaba Buhari zai halarci bikin rantsar da Mahamat Idriss Deby a matsayin shugaban rikon kwarya na Jamhuriyar Chadi

0 79

A yau, 10 ga Oktoba, 2022, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci bikin rantsar da Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban rikon kwarya na Jamhuriyar Chadi na tsawon shekaru biyu.

Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya.

Ya ce bikin da za’a gudanar da shi ne a babban birnin kasar N’Djamena, zai kara nuna karfin tattaunawa kan komawar tsarin dimokradiyya cikin lumana.

Sabon shugaban kasar yahau mulki ne bayan rasuwar mahaifinsa kuma tsohon shugaban kasar, Idriss deby Itno a watan Afrilun 2021.

Kakakin shugaban kasa Muhammad Buhari, Malam Garba Shehu yace Buhari zai dawo gida Najeriya da zarar an kammala bikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: