Gwamnatin tarayya ta ce bata biya kosisi ba wajen sakin fasinjoji 23 da aka yi garkuwa da su

0 66

Gwamnatin tarayya ta ce bata biya kosisi ba, wajen sakin fasinjoji 23 da aka yi garkuwa da su a harin da Yan bindida suka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022.

Da yake magana da manema labarai jiya a Abuja, Ministan Sufuri, Mista Muazu Sambo, ya ce fasinjojin da aka sako tuni suka gana da iyalansu bayan an duba lafiyarsu.

Ministan wanda ya bayyana farin cikinsa da sakin wadanda lamarin ya rutsa da su, ya bayyana cewa manufar gwamnati ita ce a kubutar da wadanda lamarin ya shafa lafiya ba tare da an biya kudin fansa ba.

Ya kara da cewa akwai shirye-shiryen sake dawo da zirga-zirgar jiragen kasa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a kwanan nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: