Sojin Nigeria Sun Samu Nasarar Kashe Wasu Jagororin Yan Fashin Daji Biyu

0 123

Dakarun sojin Najeriya sun ce sun samu nasarar kashe wasu jagororin ‘yan fashin daji biyu tare da kwace makamai da harsasai da kuma wasu kayyaki.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin na Tuwita ta ce jami’anta sun kama yaron ‘yan fashin ne a lokacin da ubangidan nasa ya aike shi domin sayen harsasai a cikin gari.
A cikin sanarwar da mai riƙon muƙamin daraktan hulda da jama’a na runduna ta ɗaya ta sojin Najeriya Laftanar Kanal Yahaya Musa ya fitar, ya ce sun kashe ‘yan bindigar ne sakamakon samun bayanan sirri.
Bayanan da rundunar ta samu sun nuna cewa wani fitattcen ɗan bindigar da ya addabi jihar mai suna Isiya Danwasa ya tura ɗaya daga cikin yaransa mai suna Yunusa domin sayo musu makamai da harsasai a cikin gari.
Cikin abinda rundunar ta samu sun hada babur, bindigogi 2 kirar AK 47, mujallu na bindigar AK47 guda 6, batirin chaji da kudi naira dubu 200.

Leave a Reply

%d bloggers like this: