Sojoji masu mulkin Mali sun rusa dukkan jam’iyyun siyasa a kasar

0 135

Sojoji masu mulkin Mali sun rusa dukkan jam’iyyun siyasa a kasar, matakin da aka sanar da shi a talabijin na gwamnati ranar Talata, wanda Shugaban Sojojin kasar, Assimi Goita, ya amince da shi.

Wannan na zuwa ne bayan wani taron kasa da ya bukaci a rushe jam’iyyu tare da tsawaita mulkin Goita na tsawon shekaru biyar, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a Bamako ranar 3 da 4 ga watan Mayu.

Bayan an haramta duk wani taron siyasa, ‘yan adawa sun soke wata gagarumar zanga-zanga da aka shirya yi ranar 9 ga Mayu, yayin da aka fara samun rahotannin bacewar wasu jiga-jigan ;yan siyasa. Kungiyar Human Rights Watch ta bayyana cewa wasu mutane da ba a san su ba sun kama wasu shugabannin jam’iyyu kamar su Abba Alhassane da El Bachir Thiam, abin da ke kara dagula yanayin dimokiradiyya a kasar tun bayan juyin mulkin Goita na shekarar 2020.

Leave a Reply