Tsohun gwamnan jihar Benue,ya baiyana cewa jam’iyyar PDP tana cikin mawuyacin hali da zai iya kai ta ga rushewa kafin 2027
A wata fassara ta daban kan rikicin jam’iyyar PDP, tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam, ya bayyana a tashar Arise TV cewa jam’iyyar tana cikin mawuyacin hali da zai iya kai ta ga rushewa kafin shekarar 2027 idan ba a dauki matakin gaggawa ba.
Suswam ya kwatanta halin da jam’iyyar ke ciki da marar lafiyar da ke a dakin jinya na musamman (ICU), amma ya ce akwai damar ceto idan aka yi amfani da “magani” mai karfi.
Amma kuma, wani babban lauya na jam’iyyar kuma mamba a kwamitin zartarwa, Okechukwu Osuoha, ya nuna kwarin gwiwa cewa jam’iyyar PDP za ta fito daga cikin wannan rikici da karfi idan shugabanninta suka fifita muradun jam’iyya fiye da na kansu.
Haka nan, tsohon sakataren jam’iyyar kuma mamba a kwamitin amintattu, Ibrahim Tsauri, ya ce masu son tarwatsa jam’iyyar su fice domin su bar wa ragowar mambobin da suka damu da rayuwar jam’iyyar damar sake gina ta cikin karfi da nasara kafin shekarar 2026.