Rundunar hadin gwiwa ta Arewa Maso Gabas, wato Operation Hadin Kai, ta ce dakarunta sun kashe wani babban kwamandan Boko Haram da aka fi sani da Abu Khalid, tare da wasu ’yan ta’adda goma, a dajin Sambisa na Jihar Borno.
Wannan nasara ta zo ne kasa da awanni 24 bayan dakarun bangaren Sector 1 tare da ’yan sa kai na Civilian Joint Task Force a karkashin Operation Desert Sanity sun kashe wani shahararren kwamandan Boko Haram, Julaibib, a yankin Gujba da ke cikin Timbuktu Triangle.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na hedkwatar rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar, ya ce an cimma wadannan nasarori ne a daren Asabar bayan dakarun sun yi arangama da ’yan ta’adda a yankin Komala na Karamar Hukumar Konduga.
Sanarwar ta bayyana cewa Abu Khalid na daga cikin manyan shugabannin Boko Haram, inda yake taka muhimmiyar rawa wajen tsara hare-hare da kula da harkokin sufuri da kayayyaki a yankin Sambisa.
Rundunar ta ce babu wani soja da ya jikkata ko ya rasa ransa yayin aikin, tare da jaddada cewa kwarin gwiwar dakarunta na nan daram, yayin da ake ci gaba da ayyukan share yankuna a Sambisa, Dutsen Mandara, Timbuktu Triangle da sauran maboyar Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso
A halin da ake ciki kuma, rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ’yan bindiga da dama a wani farmaki ta kasa da sama wanda aka kai sansanin shahararren jagoran ’yan bindiga, Gwaska Dan Karmi, a Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Sanarwar da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na Rundunar Sojin Najeriya a Sashe na 8, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya fitar ta ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda aka tarwatsa sansanin, aka kashe da dama daga cikin ’yan bindigar, yayin da ake ci gaba da bibiyar wadanda suka tsere domin hana su sake haduwa.