Sojoji sun samu gagarumar Nasara a Zamfara

0 207

Hukumar Sojin Najeriya tace dakarun shirin Operation Sahel Sanity sun kama wasu mutane dari da hamsin da takwas da ake zargin barayi ne a ayyukan kakkabe barayin a jihoshin Katsina da Zamfara.

Mukaddashin daraktan yada labarai na Operation Sahel Sanity, Bernard Onyeuko, ya sanar da haka yayin taron manema labarai a sansanin soji na musamman dake Faskari a jihar Katsina.

Onyeuku ya sanar da cewa dakarun wadanda suka yi aiki da bayanan sirrin da suka samu, sun fatattaki wani wajen hakar ma’adanai ta barauniyar hanya a yankin karamar hukumar Bukkuyum dake jihar Zamfara, inda suka kama barayi dari da hamsin tare da kwace bindigogi dari da ashirin.

Yace dakarun sun kuma mamayi wani sansanin barayin a yankin karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, inda suka kashe wani barawo daya tare da kama wasu biyu, kuma suka kwace bindiga samfurin AK47 guda biyu, da kwanson harsasai biyu tare da babura.

Yayi nuni da cewa an mika mutanen da ake zargin barayine ga rundunar yansandan jihar Zamfara domin cigaba da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: