STOWA ta kashe kudi fiye da naira miliyan dari biyar da hamsin da tara wajen inganta samar da ruwan sha a Jihar Jigawa
Hukumar samar da ruwansha a matsakaitan garuruwa ta jihar Jigawa STOWA ta ce ta kashe kudi fiye da naira miliyan dari biyar da hamsin da tara wajen inganta samar da ruwansha a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na 2024
Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Adamu Garba ya sanar da hakan ta cikin shirin radio Jigawa na cikar gwamnati shekara daya akan karagar mulki
Yace sun yi amfani da kudaden ne wajen gyaran gidajen ruwa 156 da kuma mayar da injiniya samarda ruwansha masu amfani da man gas zuwa hasken rana guda 19
Injiniya Adamu Garba ya kara da cewar daga watan shida na 2023 zuwa watan shida na 2024 , hukumar ta kashe kudi naira miliyan dubu daya da miliyan dari bakwai da ashirin da hudu
Manajan Daraktan yana mai cewar a shekara guda ta mulkin Umar Namadi sun gyara gidajen ruwa guda 314 akan kudi naira miliyan dari shida da tamanin, sun kuma mayar da gidajen ruwa masu amfani da man gas zuwa hasken rana guda 53 kan kudi naira miliyan dari shida da sabain
Haka kuma sun gina gidajen ruwa masu amfani da hasken rana kan kudi naira miliyan dari uku da sittin