Sule Lamido, ya bayyana cewa jam’iyyar (APC) mai mulki na iya fuskantar rarrabuwar kai nan ba da jimawa ba,

0 136

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa jam’iyyar (APC) mai mulki na iya fuskantar rarrabuwar kai nan ba da jimawa ba, inda shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, da wasu jiga-jigan jam’iyyar za su iya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa ta (PDP).

Lamido, wanda ya kasance tsohon Ministan Harkokin Waje da kuma ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan PDP, ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a babban taron PDP da aka gudanar a Aminu Kano Triangle da ke Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Rahoton Jaridar Daily Trust ya nuna cewa, da yawa daga cikin shugabannin PDP, ciki har da ‘Yan Majalisar Dattawa, gwamnoni, ‘yan majalisar wakilai da sauransu, sun sauya sheƙa zuwa APC gabanin babban zaɓen 2027.

Sai dai masu sharhi kan al’amuran siyasa sun bayyana wannan sauya sheƙa da yawa a matsayin abin da ke barazana ga dimokuraɗiyya, suna masu cewa hakan na iya janyo matsalar kafa jam’iyya ɗaya tilo a kasar. Wasu masana kuma sun yi hasashen cewa za a iya samun rikici a cikin APC sakamakon yawaitar shigowar ‘yan adawa cikin jam’iyyar kafin babban zaɓen dake tafe

Leave a Reply