Ta tabbata Anamekwe Nwabuoku shine wanda gwamnatin tarayya ta nada a matsayin sabon Akanta Janar na rikon kwarya a madadin Ahmad Idris

0 76

Awani cigaban kuma Gwamnatin tarayya ta amince da nadin Anamekwe Nwabuoku a matsayin sabon Akanta Janar na rikon kwarya na kasa.

Babban sakataren ma’aikatar kudi kasafi da tsare tsare ta kasa Aliyu Ahmed ne tabbatar da nadin, cikin wata takarda mai dauke da kwannan watan 20 ga wata Mayu na 2022, mai dauke da sa hannunsa.

Anasa bangaren tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a sabbin kafafen sada zumunta na zamani Bashir Ahmed ya tabbatar da da nadin a shafinsa na Twitter.

Sabon Akantan ana tsammanin zai kasance mai aiki cikin doka da oda, tare da nuna kwarewarsa cikin gaskiya da amana.

Nadin nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan ma’aikatar kudi kasafi da tsare tsare ta kasa ta dakatar da tsohon akanta Janar din Ahmed Idriss bisa zargin almundahanar sa ce Naira Miliyan dubu 80, kamar yanda  hukumar EFCC take zarginsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: