Tinubu Ya Ayyana Gwamnonin APC A Matsayin Shugabannin Jam’iyya A Jihohinsu

0 143

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana ainihin shugabannin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihohi daban-daban na ƙasar nan.

Da yake jawabi a wajen tarbar Gwamna Agbu Kefas na Jihar Taraba a hukumance a birnin Jalingo, Tinubu ya ayyana cewa APC tana ƙarƙashin jagorancin kowane gwamnan jiha a faɗin tarayyar Najeriya.

Shugaban ƙasar, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya ce Gwamna Kefas yanzu shi ne shugaban APC a Jihar Taraba, sakamakon sauya sheƙarsa daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Tinubu ya sake jaddada ƙudirinsa na mara wa gwamnan da majalissarsa baya domin kawo ci gaba a Jihar Taraba.

A cewarsa, gwamnan na ƙoƙarin haɗa kan al’ummar jihar tare da daidaita bambance-bambancensu domin cimma haɗin kai.

“Ina kira ga dukkan al’ummar Taraba da su mara wa gwamnan baya tare da taimaka masa ya yi nasara,” in ji shi.

“Ina farin ciki da shigowar wani gwamna daga yankin Arewa maso Gabas, kuma ina so Adamawa da Bauchi su ma su shigo jam’iyyar da ke kan mulki,” in ji shugaban ƙasar.

Leave a Reply