Tinubu ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara ɓullo da ƙwararan matakan tallafa wa Najeriya

0 238

Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara ɓullo da ƙwararan matakan tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci, saboda mummunar iillarsa ga zaman lafiyar duniya da yadda yake tarwatsa mutane da ƙara haifar da fatara.

Ya yi wannan kira ne lokacin da yake jawabi yayin ganawa da ƙaramin sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya kan yaƙi da ta’addanci, Mista Vladimir Voronkov, a fadar gwamnati.

Shugaba Tinubu ya nunar da cewa ta’addanci ya yi ta mayar da hannun agogo baya ga harkokin ci gaban ƙasa da janyo ƙarin rashin kwanciyar hankali a tsakanin iyalai da al’ummomi, amma ayyukan haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya wajen tunkararsa, sun kasance a tsittsinke kuma ana samun katsewar irin wannan tallafi ga ƙasashe masu tasowa.

Da yake yaba wa gudunmawar Najeriya ga ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci a duniya, ƙaramin sakataren na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce tuni Najeriya ta fitar da tsari a kan riga-kafi da dankwafewa da sulhuntawa, inda ya nanata yabo a kan ƙoƙarin da ƙasar ta yi zuwa yanzu don murƙushe ta’addanci. Vladmir Voronkov ya kuma faɗa wa shugaban na Najeriya cewa Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin gudanar da wani Taron Ƙoli kan Yaƙi da Ta’addanci a Abuja cikin watan Afrilun 2024.

Leave a Reply

%d bloggers like this: