Kwamitin albarkatun man fetir na jihar Jigawa ya yabawa wasu gidajen sayar da man fetir guda biyu a garin Kazaure bisa yadda suke sayar da mai ga masu ababan hawa cikin tsari mai kyau
Gidajen man sun hadar da na NBY da kuma na Alhaji Umaru Jeme petroleum Kazaure.
Shugaban kwamitin sayar da man fetir na jiha, mai ritaya Kanal Muhammad Alhassan ya yi wannan yabo a lokacin da tawagar kwamitin ta ziyara gidajen main a garin Kazaure
Yace gidajen man guda biyu sun yi fice a jihar nan wajen sayar da mai bisa cancanta da kuma tsari
A gidan main a BNY , shugaban kwamitin ya bukaci a samar da ma-aunin mai ganin yadda gidan man yake sayar da man ga masu ababan hawa da yawa domin kin yin hakan zai sanya su rinka hasara
Ya kuma gargadi wasu gidajen man fetir uku dasu gyara litocinsu na sayar da mai ko kuma su gamu da fushin kwamitin. Haka kuma tawagar kwamitin ta kai ziyara zuwa wasu gidajen man a garin.