Tinubu Ya Gana da Sabbin Hafsoshin Tsaro

0 460

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro da ya nada kwanan nan, a wani zama da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Litinin, 27 ga Oktoba, 2025.

Hafsoshin, waɗanda suka isa fadar da ƙarfe 4:00 na yamma cikin motar Mercedes-Benz Sprinter tare da rakiyar Toyota Land Cruiser, sun shiga ganawar da Shugaban Ƙasa a forecourt na Aso Rock.

Ganawar ta ɗauki kusan mintuna 40, inda suka fita da ƙarfe 4:40 na yamma bayan kammala taron.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da:

1. Laftanar Janar Olufemi Oluyede – Babban Hafsan Tsaro

2. Manjo Janar W. Shaibu – Babban Hafsan Sojoji

3. Rear Admiral I. Abbas – Babban Hafsan Rundunar Ruwa

4. Air Vice Marshal S.K. Aneke – Babban Hafsan Rundunar Sama

5. Manjo Janar E.A.P. Undiendeye – Babban Daraktan Leken Asiri na Tsaro

Tinubu ya nada sabbin hafsoshin ne a ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025, domin ƙarfafa tsarin tsaro na ƙasa. Sabbin hafsoshin sun maye gurbin tsofaffi da suka jagoranci rundunonin tun daga shekarar 2023.

Shugaban Ƙasa ya bayyana godiya ga hafsoshin da suka sauka, musamman Janar Christopher Musa, bisa jajircewarsu, tare da jaddada kira ga sabbin shugabanni da su tabbatar sun inganta, tsaro, ƙwarewa da haɗin kai a cikin rundunonin sojin ƙasar.

Leave a Reply