‘Yan Ta’adda Na Barazanar Kai Hari Majalissar Walikai – in ji Garba Diso

0 473

Shugaban kwamitin tsaron cikin gida na majalisar wakilai, Hon. Garba Muhammad Ɗiso, ya bayyana cewa sun samu barazanar harin bama-bamai daga ‘yan ta’adda a ginin majalisar dokoki ta tarayya.

Ɗiso ya bayyana hakan ne yayin taron sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudirin dokar kafa Hukumar Tsaron Majalisar Dokoki, wadda za ta tabbatar da tsaron ‘yan majalisa, ma’aikata da baki masu zuwa majalisar.

Ya ce majalisar ta dade tana fuskantar matsalolin tsaro da suka hada da satar motoci da babura, lalata kayan gwamnati, amfani da katin karya, da kuma shigowar baki ba tare da izini ba cikin harabar majalisar.

Hon. Ɗiso ya jaddada cewa akwai bukatar karfafa tsaron majalisar domin kare rayuka da dukiyoyi, tare da hana duk wani abu da ka iya barazana ga tsarin dimokuradiyya a ƙasar.

Leave a Reply