Tinubu ya kara tsawaita ziyarar da yake yi a nahiyar Turai

0 539

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kara tsawaita ziyarar da yake yi a nahiyar Turai, kamar yadda jaridar *Daily Trust* ta ruwaito. 

Wannan yana zuwa ne a lokacin da jam’iyyar hamayya ta PDP da sauran shugabannin hamayya ke sukar rashin kasancewar shugaban kasar a cikin kasar, a lokacin da ake fama da rikice-rikice a wasu sassan Najeriya. 

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nemi shugaban kasar ya dawo daga ziyarar, yana mai cewa lamarin da ake fuskanta a Jihohin Plateau da Benue na bukatar kulawarsa. 

Haka kuma, dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana cewar a wannan dai-dai lokacin da shugaban ke tafiye-tafiye, an kashe mutane da dama a Najeriya, wanda ya kamata ya dawo domin daukar mataki.

Leave a Reply