Tsadar kayan masarufi ta ragu a Najeriya da kaso 15.4 cikin 100 a watan Nuwamba
Tsadar kayan Masarufi ta ragu a Najeriya da kaso 15.4 cikin 100 a watan Nuwamba, fiye da baya da kaso 15.99 cikin watanni 9 da suka gabata.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ita ce ta bayyana hakan cikin wani rahoto da ta fitar a jiya.
Rahotan ya yi nuni da cewa ana samun saukin tsadar kayan masarufi tun daga watan Maris na wannan shekara, inda tsadar take a mataki na 18.17
Hukumar ta NBS a rahotan ta, ta yi nuni da cewa kayayyaki sunyi tsada a Maraya da kaso 15.92 daga watan Nuwamba na 2020 zuwa 2021.
Kazalika, hukumar ta ce tsadar kayayyaki a kyauyika ta sake hawa da kaso 14.89 a watan Nuwamba sabanin kaso 14.33 da ake dasu a watan Nuwamba na 2020.