Tsaro da N234 farashin mai: shin da gaske ‘yan najeriya na kunyar caccakar Buhari?

0 96

Lokacin da shugaba Buhari ya dare kujerar mulki a shekara ta 2015, ya gaji farashin litar man fetir akan naira 87 amma yanzu ana sayar da ita naira 165 kuma ana hangen za a kara farashin man a kwanan nan.

Yaki da ayyukan rashawa da ta da komadar tattalin arziki da kuma wanzar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya su ne ginshikan da shugaba Muhammadu Buhari ya girka gwamnatinsa bayan karbar madafun iko daga hannun tsohon shugaba Goodluck Jonathan a watan Mayu na shekara 2015.

Gabanin zaben, sai da shugaba Buhari ya kwashe watanni yana yawon neman kuri’ar ‘yan kasar, inda a lokuta daban-daban ya yi alkawarin tabbatar da tsaro da yaki da tsadar rayuwa ta hanyar saukaka farashin albarkatun mai na kasar da kuma kayayyakin masarufi na yau da kullum.

Misali, batun murkushe mayakan Boko Haram domin wanzar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin kasar na daga cikin laffuzan kamfe na shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar ta APC.

Sai dai, shekaru shida bayan kafa gwamnati, cabewar al’amura a Najeriya na ci gaba da daukan salo iri-iri, musamman a bangarorin tsaro da tattalin arziki da zargin aikace-aikacen rashawa da cin hanci a sassa da cibiyoyin gwamnati – da ma yanayin zamantakewa a tsakanin ‘yan kasar.

Matsalar sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa, fadace-fadace masu nasaba da addini ko kabilanci ko kuma bangaranci, tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki, musamman kayayyakin masarufi a kasuwannin kasar da hauhawar farashin kudaden musaya na ketare da na litar albarkatun mai a kasar na ci gaba da dagula lissafin rayuwar ‘yan Najeriya karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Alal misali, lokacin da shugaban ya dare kujerar mulki a shekara ta 2015 ya gaji farashin litar man fetir akan naira 87 amma yanzu ana sayar da ita naira 165 baya ga yunkurin baya-bayan nan da gwamnatinsa ta yi na kara farashin zuwa naira 200 ko da yake, daga bisani kamfanin mai na kasar ya janye karin.

“Na yi mamaki matuka a ce ana neman sayar da litar mai naira 200 a Najeriya karkashin gwamnatin Buhari, mutumin da ya ce mana muddin muka sayi litar mai sama da naira 50, to babu shakka mu talakawa an cuce mu”, inji Bashir Mohammed Yakasai wani direban babur din A-daidaita-Sahu a Kano.

“Ni yanzu ba abin da zancewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, domin iya tsada da wahalar rayuwa ina ganin ta, don haka in ya so ma ya kai farashin mai fiye da naira 200, saboda mu talakawan Najeriya mun saba da wuya, kawai addu’ar mu Allah ya ba mu abin saya” a cewar wani magidanci a Kano Musa Bello Bichi.

To amma tsohon mataimakin shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC Comrade Isa Tijjani ya ce muddin gwamnati na muradin rage farashin mai, tilas sai ta gyara matatun tace mai mallakar ta – wato matatar mai ta garin Fatakol, Kaduna da Warri.

Baya ga haka, sai an dauki matakan daidaita farashin musayar kudin ketare wato Dollar da kuma mayar da hukumar da ke kayyade farashin mai a Najeriya wato PPPRA karkashin fadar shugaban kasa, maimakon zamanta a karkashin kulawar kamfanin mai na NNPC.

Ta fuskar tsaro kuwa, yayin da gwamnatin ba ta kai ga murkushe ayyukan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar ba, matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a yankin arewa maso yammaci da tsakiyar kasar, baya ga tashin hankalin kabilanci da ke wakana a yankunan kudancin kasar ta Najeriya.

Kazalika, zarge-zargen rashawa da cin hanci a karkashin gwamnatin ta shugaba Buhari na ci gaba da karuwa.

Zargin facaka da kudi a hukumar raya yankin Niger Delta ta NDDC da na zargin batan dabo da kudaden sayo makamai da mai baiwa shugaban shawara kan sha’anin tsaro, Babagana Munguno, ya ambata a kwanakin baya, ya yi daidai da zargin da aka yi wa gwamnatin shugaba Jonathan na cin kudin makamai da kuma facaka da kudin albarkatun mai a wancan lokaci.

Mai baiwa shugaba Buhari shawara a fannin tsaro, Babagana Munguno
Mai baiwa shugaba Buhari shawara a fannin tsaro, Babagana Munguno

Kazalika, masu kula da lamura na cewa, har yanzu yadda ministocin gwamnati ke tafiyar da rayuwarsu, da ‘yan majalisar dokoki da sauran masu rike da mukaman siyasa a kasar, ba shi da wani banbanci a zo a gani da yadda al’amura suka wakana a gwamnatocin baya.

Bugu da kari, yanayi da salon tafiyar da ayyukan gwamnati a matakin jihohin da Jam’iyyar APC ke mulki ba shi da banbanci da na jihohin Jam’iyyar hamayya PDP.

“Gwamnatin Buhari ta samu alfarma a wurin ‘yan Najeriya ta hanyoyi da dama, kuma a iya cewa, babu wata gwamnati da ta samu irin wannan tagomashi a tarihin Najeriya,” in ji Comrade Abdulrazak Alkali guda cikin ‘yan gwagwarmayar shugabanci na gari a Najeriya.

Dangane da batun karin farashin albarkatun mai kuwa, Comrade Alkali ya ce kada ‘yan Najeriya su sakankance, alamu sun nuna tun da gwamnati ta fara yunkurin kara farashin babu abin da zai hana ta, magana ce ta lokaci kawai.

Gwamnatin tarayya ta Jam’iyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta da kuma gwamnatocin jihohi na Jam’iyyar sun ci gajiyar hamayya, amma su ba sa juriyar hamayya, a cewar comrade Kabiru Sa’idu Dakata, mamba a gamayyar kungiyoyin fararen hula na Kano.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP a 2019, Atiku Abubakar
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP a 2019, Atiku Abubakar

“Wanzami ba ya son Jarfa, gaskiyar lamari hamayya ta tabarbare a karkashin gwamnatin APC ta Muhammadu Buhari, ana yi wa ‘yan hamayya barazana, duk da cewa, tarihi ya nuna shugaba Buhari ya taba shiga zanga zangar yaki da karin farashi a kasar nan kuma ya yi kiraye-kirayen shugaba ya sauka saboda gazawarsa, amma yanzu a gwamnatinsa idan ka yi duk wani na suka mai ma’ana game da manufofi da tsare-tsaren gwamnati karkashin inuwar NGO ko Jam’iyyar siyasa ko kuma dan kasa, sai kawai a ce kai makiyin gwamnati ne.”

Sai dai Alhaji Abdulkarim Dayyabu, guda cikin magoya bayan shugaba Buhari na cewa, ya kamata a yi wa shugaban uziri, la’akari da yadda ya karbi gwamnati cikin dinbin kalubale.

“Ya kamata ‘yan Najeriya su yi wa shugaban uziri domin ya samu kasar cikin mawuyacin hali kuma sha’anin gyara abu ne mai wahala”

Shi ma Alhaji Mukhtar Gidado, daya daga cikin dattawan arewa, na da irin wannan fahimtar.

“Babban kalubalen shugaba Buhari shi ne, ya zama kamar shi kadai ne tilo ke da zuciyar daidaita al’amura a cikin gwamnatin, domin akwai alamu na abu mai kama da zagon kasa daga wasu daga cikin jami’an gwamnatin kuma ga ‘yan siyasar hamayya su ma ba su bar shi ba.”

Sheikh Ahmed Gumi tare da Fulani 'yan bindiga a kokarin shiga tsakani da yake yi
Sheikh Ahmed Gumi tare da Fulani ‘yan bindiga a kokarin shiga tsakani da yake yi

‘Yan Najeriya dai na ci gaba da kokawa game da matsalar tsaro da durkushewar tattalin arziki da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da karuwar zargin cin hanci da rashawa a matakan gwamnati daban-daban na gwamnatin Jam’iyyar APC da tsarin siyasar uban-gida da zargin amfani da kudi da jami’an tsaro wajen gudanar da zabuka da sauran al’amura na rashin ci gaba.

Amma duk da haka, mizanin suka da hamayya da kalubalen gwamnatocin baya suka fuskanta daga ‘yan kasa kungiyoyi da hukumimin ciki da wajen Najeriya ya zarce wadda ake yi wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a yanzu.

Comrade Yahaya Shu’aibu Ungogo wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Najeriya ya fayyace dalilan da suka sanya mizanin caccakar gwamnatin Buhari ya yi kasa.

“Na farko har yanzu Buhari na da sauran kimi a idon wasu daga cikin ‘yan Najeriya,don ba sa caccakar sa, duk da cewa, sunyi ammana cewa, har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, abu na biyu kuma kusan kowa mai laifi game da gazawar gwamnatin, tunda kowane rukuni na al’uma ya bada gudunmawa wajen korar tsohuwar gwamnati domin gwamnatin Buhari ta tabbata.”

Saboda haka, ‘yan siysa da kungiyoyin fararen hula da shugabanni addinai, da ‘yan Boko da ‘yan kasuwa da talakawa da-ma kungiyoyi da cibiyoyi da gwamnatocin kasashen ketare, duka sun taka rawa wajen kafa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Saboda haka dukkanin su suna kunyar su soke gazawar ta, domin tamkar Burma wuka a ciki ne.”

Asalin bayanin;

https://www.voahausa.com/a/n234-farashin-mai-shin-da-gaske-yan-najeriya-na-kunyar-caccakar-buhari-/5830500.html

Leave a Reply

%d bloggers like this: