Tsawa ta salwantar da akalla gidaje 46,000 da makarantu, da dabbobi 700,000 a Vietnam

0 113

Guguwar mai taken Yagi, ita ce guguwa mafi karfi da ta yi wa arewacin Vietnam cikin akalla shekaru 30, guguwar ta lalata gidaje sama da 46,000 da makarantu da dama, dabbobi akalla 700,000 sun yi mushe sakamakon saukar tsawa.

Hukumomin birnin Hanoi sun ce guguwa ta tumbuke sama da bishiyoyi 25, 000, sun kuma toshe muhimman tituna a tsakiyar birnin, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa. Ambaliyar ta kuma tafi da kayan lambu irinsu ayaba da guava da masara wadanda galibi ana sayar da su a kasuwannin da ke kusa.

An dakatar da manyan motoci da ke tsallaka wata babbar gada a tsakiyar birnin Hanoi, tare da katse layin dogo a kan gadar “Long Bien” yayin da ambaliyar ta yi tsanani.

Hotunan da hukumomi suka wallafa a shafukan sada zumunta, sun nuna rabin gadar Phong Chau mai tsawon mita 375 ta rushe. An ceto mutane biyar da ke tsallaka gadar a lokacin farwuar lamarin, amma wasu mutane takwas sun bace, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Arewacin kasar Vietnam na da yawan jama’a kuma yankin ya kasance babbar cibiyar kera kayan fasaha a duniya ciki har da Samsung. Yanzu haka dai jami’an agaji na kokarin isowa ga mutane  da suka makale a ambaliyar, an kuma yi gargadin yuwar sake samun zabtarewar laka musamman a yankuna 401 da ke kusa da tsaunuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: