Allah Ya yi wa tsohon gwamnan jihar Oyo Alao Akala rasuwa a yau Laraba.
Marigayin wanda ya rasu yana da shekara 71. ya taɓa zama gwamnan jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya daga shekarar 2007 zuwa 2011.
Alao-Akala ɗan asalin ƙaramar hukumar Ogbomoso ta arewa ce a jihar Oyo.
Kfin ya zama gwamna, sai da ya yi mataimakin gwamna daga tsakanin Mayun shekarar 2003 zuwa Janairun 2006 duk a ƙrƙashin jam’iyyar PDP.
A shekarar 2014 ne tsohon gwamnan ya koma jam’iyyar Labour bisa hujjar cewa ana abubuwan da ba su dace ba a tsohuwar jam’iyyarsa.
A 2015 ne ya sake tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar Labour amma bai yi nasara ba.
Sannan a 2019 ya sake tsayawa takarar gwamnan a ƙrƙashin jam’iyyar ADP.