Wani dan majalisar dokoki ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da cin amanar mutane

0 102

Wani dan majalisar dokokin jihar Katsina, Aminu Garba Danmusa, ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da cin amanar mutanen jiharsa ta asali.

Aminu Danmusa, wanda ke wakiltar karamar hukumar Danmusa a majalisar dokokin, yana tsokaci kan tabarbarewar tsaro a Najeriya da karuwar hare-hare daga ‘yan bindiga a jihar Katsina da yankin Arewa maso Yamma baki daya.

A wani faifan bidiyo da wakilinmu ya gani, dan majalisar ya ce shugaban kasar ya yi watsi da mutanen jihar.

Aminu Danmusa ya kara da cewa ana kashe mutanen mazabarsa tare da sace shanu babu adadi, wadanda ‘yan bindiga suka sace saboda jami’an tsaro a yankin sun gaza.

Ya ce Shugaba Buhari zai iya kawo karshen matsalar rashin tsaro a cikin kwanaki bakwai, inda ya kara da cewa, halin shugaban kasar na cin amana ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: