Wani kazamin rikicin ‘yan bindiga ya yi sandiyyar mutuwar yan ta’adda 20 a jihar Katsina

0 300

Akalla ‘yan ta’adda 20 ne suka mutu, ciki har da fitattun shugabanni a wani kazamin rikici da ya barke tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga a jihar Katsina.

Rikicin wanda ya faru da sanyin safiyar  jiya Laraba, rahotanni sun bayyana cewa, an gwabza rikicin ne a yankin Dan-Ali da ke karamar hukumar Dan-Musa a jihar.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana rahoton rikicin a wani sharhi da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa, rikicin ya faru ne tsakanin ’yan kungiyar ta’adda ta Mai Nore da Buzaro.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, rikicin ya tsananta, inda aka dauki tsawon lokaci ana ta harbe-harbe a cikin al’umma.

An kuma bayar da rahoton cewa, ‘yan bindiga da dama sun samu raunuka yayin arangamar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: