Wani Mahaifi Ya Hallaka Dansa Mai Shekara 16 Bisa Zargin Satar Mudu 1 Na Gero

0 70

Wani yaro dan shekara 16 mai suna Mustapha Sunusi ya mutu a gidan mahaifinsa Abdulwahab Sunusi bisa zargin satar mudu guda na gero a kauyen Tanagar dake karamar hukumar Warawa ta jihar Kano.

Wani shaida ya ce, Abdulwahab ya hallaka dan nasa ne a kokarinsa na cusa tarbiyya a kan dan nasa mai shekaru 16.

Mahaifin ya dauki wannan matakin ne saboda bacin da ya ron ya cusa masa na yin sata dukda irin tarabiyar da ya bas hi.

Lamarin dai ya zo ne sa’o’i 48 bayan wani matashi dan shekara 22 ya kashe mahaifiyarsa a unguwar Rimi Kebe da ke cikin birnin Kano. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa manema labarai cewa suna nan suna gudanar da bincike kuma daga zarar sun kammala zasu kira taron yan jaridu domin sanarwa al’umma sakamakon binciken su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: