An Harbe Wani Dan Jarida A Yankin Arewa Maso Yammacin Kasar Kamaru

0 73

Wannan dai shi ne kisan dan jarida na uku a kasar cikin wannan shekara.

Rahotanni sun ce Anye Nde Nsoh na cikin wata mashaya a birnin Bamenda lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka bude wuta.

Anye Nde Nsoh ya yi aiki da jaridar mako-mako ta Advocate kafin rasuwar sa.

Bamenda dai na daya daga cikin yankunan da rikici yake shafa na tsawon shekaru da suka hada da ‘yan aware masu magana da Ingilishi.

Amma sauran ‘yan jaridar Kamaru biyu da aka kashe a ‘yan watannin nan sun mutu a babban birnin kasar, Yaoundé.

Leave a Reply

%d bloggers like this: