Ya Kamata Gwamnati A Kowane Mataki Ta Gaggauta Bayar Da Fifiko Kan Harkokin Kiwon Lafiya

0 61

Kungiyar likitoci ta kasa ta ce ba da fifiko wajen samar da kudade ga bangaren kiwon lafiya daga dukkan matakai na gwamnatoci yana da matukar muhimmanci wajen kawo karshen yadda ma’aikatan lafiya ke barin kasarnan.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a jiya bayan taronta na shekara-shekara karo na 63 da ta gudanar a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Sanarwar ta samu sa hannun shugaban kungiyar, Dr Uche Ojinmah da Sakatare Janar na kungiyar, Dr Jide Onyekwelu.
A cewar sanarwar, ya kamata gwamnati a kowane mataki ta gaggauta bayar da fifiko kan harkokin kiwon lafiya, da nuna kyakkyawar jajircewar siyasa wajen samar da kudaden kiwon lafiya da kuma biyan albashi mai kyau da inganci.
Ta yi kira da a samar da ingantaccen yanayin aiki mai kyau, da sake fasalin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi, da samar da ababen more rayuwa da kuma bayar da karin damammaki ga likitoci a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: