Wasu Sojoji Dauke Da Makamai Sun Mamaye Harabar Wani Ofishin NDLEA Dake Jihar Jigawa

0 78

Wani lamari mai hatsari ya kusa aukuwa a ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA dake jihar Jigawa a jiya da safe bayan da wasu sojoji dauke da makamai suka mamaye harabar ofishin a kokarin kubutar da wani soja da aka kama bisa zarginsa da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Lamarin ya haifar da firgici a tsakanin mazauna unguwar G9 Quarters inda ofishin hukumar NDLEA yake.
Wani mazaunin unguwar, Haruna Idris, ya ce sojoji kimanin goma ne suka mamaye ofishin hukumar ta NDLEA ta hanyar amfani da sanduna da sauran muggan makamai a kokarinsu na ceto abokin aikinsu da ke tsare a hannun hukumar ta NDLEA.
An kama sojan ne a ranar Lahadin da ta gabata tare da wasu abokan harkarsa bisa zargin sayar da muggan kwayoyi a Gindin Dinya, wani waje da ake yawan samun rikici a birnin.
Da aka tuntubi kakakin hukumar ta NDLEA a jihar Jigawa, Jerry Mathew, ya shaida wa manema labarai cewa ba a yi masa bayani ba game da lamarin, kuma ya ki yin karin haske, yayin da aka kasa jin ta bakin rundunar sojoji ta jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: