Yara 8 Ne Ake Fargabar Sun Mutu Sakamakon Hatsarin Kwale-Kwale A Jihar Zamfara

0 78

Yara 8 ne ake fargabar sun mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a lokacin da suke tsallaka kogi a cikin wani jirgin ruwa a birnin Gusau na jihar Zamfara.

An rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a Gadar Berger da ke unguwar Tullukawa a Gusau, babban birnin jihar.

An kuma bayar da labarin cewa mazauna yankin a kodayaushe suna tsallaka kogi domin samun gurbataccen ruwa saboda rashin ruwa da ake fama da shi a babban birnin jihar.

A cikin wani faifan bidiyo da masu aiko da rahotanni suka samu, wani mutum mai suna Shehu Hamza wanda da ya shaida lamarin, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon lodin da ya wuce hankali da matukan jirgin ruwan suka yi.

Ya ce lamarin na baya-bayan nan shi ne karo na uku a cikin jerin hadurran kwale-kwale da aka samu a kogin.

Da aka tuntubi mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace har yanzu bai samu cikakken bayani ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: