Wasu ‘Yan Bindiga Sun Saki Faifan Bidiyon Wadanda Sukayi Garkuwa Dasu Suna Kukan Neman Agaji

0 64

Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da wata dalibar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Zamfara da ke Gusau, Ummulkhairi Musa, tare da wasu mutane biyar sun fitar da wani faifan bidiyo na wadanda suka yi garkuwa da su suna kukan neman agaji a cikin wani daji.

An bayar da labarin cewa an sace ‘yan matan ne a hanyar Birnin Magaji zuwa Kaura Namoda a ranar 15 ga watan Janairu, 2023, yayin da suke dawowa daga wani bikin aure.

Ummulkhairi Musa, wacce daliba ce ta ajin karshe, an ce an sace ta ne a lokacin da ta ke shirin rubuta jarabawar karshe.

A cikin faifan bidiyon, an ga wani matashin dan ta’adda dauke da bindiga kirar AK-47 a kafadarsa yana dukan wadanda suka kama da bulala yayin da suke neman a taimaka musu.

Da yake zantawa da manema labarai, wani ma’aikacin kwalejin, Jamil Musa, ya ce duk kokarin da aka yi na ganin an sako Ummulkhairi Musa da sauran wadanda aka sace ya ci tura. Da aka tuntubi mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya ce ana ci gaba da kokarin kubutar da wadanda aka kama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: