Wani Shaida Ya Faɗawa Kotu Yadda APC Tayi Maguɗi a Zaɓen Shugaban ƙasa a Jigawa

0 157

Wani shaidar jam’iyyar PDP, Mohammed Tata ya faɗa wa Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasa cewa tilasta masa aka yi ya sa hannu a wani kwafin sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa na 2019.

Tata ya yi iƙirarin cewa an razana shi da cewa za a kore shi daga Shirin N-Power inda yake aiki idan ya ƙi sa hannu a sakamakon.

Shaidar ya ƙara faɗa wa Kotun cewa ya kai rahoton wannan razanarwa da aka yi masa, amma ba a yi wa waɗanda suka razana shi ɗin komai ba.

A ranar Litinin ɗin nan ne, 8 ga watan Yuli, 2019 Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasar ta saurari wannan shaida, Mohammed Tata.

Tata ya faɗa wa Kotun, wadda ke duba ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta, Atiku Abubakar suka shigar a zaɓen shugaban ƙasa cewa an tilasta masa ya sa hannu a sakamakon zaɓen ne a wata tashar zaɓe a Jihar Jigawa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Tata ya yi aiki a matsayin wakilin jam’iyyar PDP a Jigawa a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.Yayinda lauyan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, Yunus Usman ke tambayar sa a Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Shugaban Ƙasar dake Abuja, wakilin na PDP ya ce: “An kunyata ni, kuma an tsorata ni inda na sa wa sakamakon hannu bisa tilas.“An faɗa min cewa idan na ƙi sa hannu, za a cire sunana daga Shirin N-Power”.

Ya ƙara yin iƙirarin cewa ƙuri’a 700 da Buhari da jam’iyyar APC suka ce sun samu, ba za su iya bada hujjar samun nasu ba, saboda “babu wani cin zaɓe saboda ba a yi zaɓe ba”.Shaidar, wanda ya ce shi Musulmi ne wanda ya yi imani da ƙaddara, ya ce bai damu jam’iyyar PDP ko APC ta ci zaɓe a mazaɓar tasa ba.

Amma ya ƙara da cewa: “Ni abinda nake so shi ne ina buƙatar adalci a ƙasata. Ban damu ba ko jamiyyata ta ci zaɓe ko ta faɗi, amma ba na farin ciki da abinda ya faru”.Ya faɗa wa lauyan INEC da Kotun cewa ba a ba shi kwafin sakamakon ba saboda babu zaman lafiya a yankin lokacin zaɓen.

Lauyan APC, Lateef Fagbemi ya tambaye shi me yasa bai ambaci sunayen mutanen da suka yi masa barazanar ba a jawabinsa na rantsuwa.A amsar da ya bayar, Tata ya ce ya ƙi ambatar sunayen ne saboda dalilan tsaro, da kuma duba da cewa har yanzu yana aiki da N-Power.

Leave a Reply

%d bloggers like this: