Labarai

Wani Sufetan Dan Sanda ya kashe abokan aikin sa 2 tare da raunata wasu mutane 4 ciki harda sirikin sa a Kwalegin Yan sanda ta Maiduguri da ke jihar Borno

Wani Sufetan Dan Sanda Bello Abdullahi, ya kashe Yan sanda 2 abokan aikin sa, tare da raunata wasu mutane 4 ciki harda Sirikin sa a Kwalegin Yan sanda ta Maiduguri da ke Jihar Borno.

Wani shaidar gani da Ido, ya fadawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba da Daddare.

Wani daga cikin Makotansa, wanda ya bukaci a sakaya sunan sa, ya fadawa manema labarai cewa Mutumin ya jima yana samun rashin Jituwa da Matarsa, da kuma Sirikin sa, inda kuma Jami’an yan sanda suke ta kokarin sansata su.

An bada rahotan cewa Matar Jami’in ta tafi gidan su, domin ta ji da abinda yake faruwa a tsakanin ta da Mijin ta.

Hakan ce ta sa Mijin ya Kunna Wuta domin kone gidan sa da kuma gidajen Sirikin sa da na Abokan aikin sa wanda suke shiga Tsakani, tare da kashe mutum 2 a lokacin.

Tuni aka kama mutumin kuma aka tsare shi a Ofishin yan sandan dake cikin Kwalegin.

Gidan Talabajin na Channels Tv, ya yi kokarin tuntubar Kakakin yan sandan Jihar Borno, amma abin ya ci tura.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: