Wasu Ƴan Sanda Sunyi Aika-Aika Har An Rasa Rai a Jigawa

0 257

Rundunar yan sandan jiharnan ta tabbatar da bige wata mata mai suna Hauwa Danladi Turis, da wasu mutane 4, wanda jami’anta sukayi da motor rundunar, da yayi sanadi rasa ranta, tare da jikkata mutane 4 magashiyyan.


Kakakin rundunar Abdu Jinjiri, shi ne ya shaida hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, inda yace lamarin ya auku ne a ranar juma’a, cikin karamar hukumar malamadori.


Yace lamarin ya auku ne, yayin da jami’an rundunar ke kokarin shawo kan wani ma mota da ake zargi da laifi, sai dai yace a yanzu haka am tsare yan sandan da suka bige mutanen, kuma ana gudanar da bincike akai.

Dayake nuna alhininsa a kan lamarin, shugaban karamar hukumar Alhaji Bako Kashin Dila, yayi kira da jama’a su kwantar da hankulansu yayin da ake cigaba da gudanar da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: