EFCC Ta Kama Dan Wani Gwamna

0 85

Hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zakon kasa EFCC tace ta kama dan gidan tsohon gwamnan jihar Kogi marigayi Abubakar Audu, wato Muhammad Audu.

Mukaddashin mai magana da yawun hukumar Tony Orilade ya bayyana cewa an kama Muhammad Audu ne bisa zargin sa akan wasu kudade na bayar da makudan dalolin Amurka da kuma bilyoyin nairori ga kungiyar kwallon kafa ta Najeriya.

Ya kara da cewa bincike ya nuna cewa yana amfani da kamfanonin sa guda biyu wajan nuna kudaden da baze iya samun suba.

Hukumar ta sanar da cewa nan gaba kadan za’a mika wanda ake zargin zuwa kotu da zarar ta kammala binciken ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: