Tsauraran Hukuncin Da Ya Kamata Buhari Ya Dauka Kan Gwamnonin Arewa – Sultan

0 225

Mai martaba sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki mataki kan gwamnonin da suka gaza dakile matsalolin al’umarsu, da suka hadar da barace-barace, mace macen aure, shaye shaye da sauransu.

Sarkin musulmin, yayi wannan kiran ne a yayin jawabin sa a matsayin  shugaban taron majalissun addinin musulunci na Najeriya, wanda uwar gidan shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari ta shirya, mai taken sabon Muhallin iyalan Musulmai.

A nata jawabin Aisha Buhari ta bayyana  cewa taron zai taimaka wajen fahimtar da iyaye sauke nauyin da ke wuyansu, na kula da iyayan su, musamman almajirai da ake tura su yankuna daban daban a fadin kasar nan.

Shima a nasa jawabin Shugaban majalissar Dattijai Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya bayyana cewa ma’aikatar ilimi ta kasa zatayi duk mai yiwuwa wajan tilasata iyaye da suna kai yayan su  makaranta, tare da cewa gwamnati kadai,bazata iya magance matsalolin ba tare da goyon bayan malaman addinai ba da kuma masu masarautun gargajiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: