Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu fasinjojin da ba a tantance adadinsu ba a cikin wata motar bas a jihar Kogi

0 70

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi garkuwa da wasu fasinjojin da ba a tantance adadinsu ba a cikin wata motar bas mai kujeru 18 a garin Ochadamu da ke karamar hukumar Ofu a jihar Kogi.

A cewar manema labarai, motar bas din da aka ce ta nufi Abuja ne daga yankin kudancin kasarnan, an kai mata harin ne a wani wurin da ake garkuwa da mutane a kan hanyar.

Majiyoyi a yankin sun bayyana cewa sace-sacen mutane a garin Ochadamu ya ragu matuka amma ya sake dawowa sosai a ‘yan kwanakin nan bayan da aka wargaza shingayen binciken sojoji da ke yankin sakamakon wani mummunan hatsarin da ya faru a babbar hanyar.

An rawaito cewa jami’an tsaro da suka hada da ’yan banga a yankin sun yi ta kokarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su tun bayan faruwar lamarin.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin a jiya, mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Jerry Omodara, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na daf da shawo kan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: