An bayar da kwangilar ginawa da gyaran gidajen samar da ruwan sha masu amfani da hasken rana a karkashin ayyukan ‘yan majalisa na jihar Jigawa

0 60

Hukumar samar da ruwan sha a kananan garuruwa da tsaftar muhalli ta jihar Jigawa (STOWA) ta shirya bikin bude tayin bayar da kwangilar ginawa da gyaran gidajen samar da ruwan sha masu amfani da hasken rana a karkashin ayyukan ‘yan majalisa.

Manajin Daraka na hukumar, Engineer Adamu Garba, yace ayyukan da za a gudanar sun hada da gina sabbin gidajen samar da ruwan sha masu amfani da hasken rana guda 38 da daga darajar wani gidan ruwa guda 1 da kuma gyaran wasu gidajen samar da ruwan sha masu amfani da hasken rana guda 19.

Ya kara da cewa za a gudanar da dukkan ayyukan a mazabu 14 kuma za a kashe kudi sama da naira miliyan 350 a ayyukan.

Da yake jawabi, wakilin hukumar duba ayyuka Due Process, Injiniya Alhassan Abbas, yace hukumar za ta tabbatar da cewa an bayar da ayyukan ga kamfanonin da za su gudanar da ayyuka masu kyau da inganci, inda ya hori kamfanonin da suka samu nasara da su kiyaye da dokoki wajen gudanar da ayyukansu. Sauran wadanda suka yi jawabi sun hada da wakilan kwamitin ruwa na majalisar dokoki da kungiyoyin fararen hula.

Leave a Reply

%d bloggers like this: