Jihar jigawa itace wacce tafi karancin masu dauke lalurar cuta mai karya garkuwar jiki a Najeriya

0 81

An bayyana Jihar jigawa a matsayin wacce take da karancin masu dauke lalurar cuta mai karya garkuwar a tsakanin takwarorinta na fadin kasar nan.

Babban jami’in hukumar dake dakile yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki a jihar Jigawa, Malam Ibrahim Almajiri ya bayyana haka ta cikin shirin Radiyo Jigawa na musamman, dangane da ranar masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki ta duniya.

Ibrahim Almjiri ya ce an samu nasarar ne bisa yadda gwamnati take taimakon masu dauke da cutar a fannoni daban daban domin yaye musu radadi da kuma inganta rayuwar su.

A jawabinsa, shugaban kungiyar masu dauke da laurarar cuta mai karya garkuwar jiki, Malam Abubakar Ibrahim ya ce sukan fuskanci kalubalen a cikin al’umma tare da shawartar mutane da su kiyaye kalubalantar masu dauke da cutar.

Abubakar Abdullahi ya kuma yabawa gwamnatin jiha bisa irin tallafin da ta basu domin kula da lafiyar su.

Ya shawarci masu lalurar da su cigaba da zuwa asibitoci domin gwaji da kuma shan magani da nufin kaucewa yaduwar cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: