Kwararan dalilai ne suka sa na janye karar da nake yiwa Aminu – Aisha Buhari

0 97

Matar Shugaban kasa Aisha Buhari ta janye ƙara da kuma tuhumar da take yi wa ɗalibin nan Aminu Muhammad, kamar yadda lauyansa ya sanar da haka.

Cikin wani saƙon da ya fitar lauyan ta bai yi ƙarin bayani ba game da dalilin da ya sa Aisha ta janye ƙarar.

Matakin na zuwa ne bayan ɗalibin ya shafe kwana uku a gidan yari da ke Suleja bisa umarnin kotun.

A ranar Litinin ake sa ran ci gaba da zaman kotun don sauraron neman beli da lauyan Aminu ya yi a zaman ranar Talata da aka yi, wanda bai yi nasara ba.

Matar shugaban na zargin Aminu da ɓata mata suna saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter tare da maƙala hotonta yana cewa  ta ci kuɗin talakawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: