Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin Najeriya da kada su nuna bangarancin siyasa da kuma kokarin ganin an samu nasarar zaben 2023

0 90

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin Najeriya da kada su nuna bangarancin siyasa da kuma kokarin ganin an samu nasarar zaben 2023.

Shugaban kasar ya bayar da wannan umarni ne a jiya yayin da yake bayyana bude taron shekara-shekara na Hafsan Sojoji na bana da aka gudanar a Sokoto.

Shugaban kasar ya ce ya zama wajibi rundunar soji ta tallafa wa hukumomin farar hula ta hanyar samar da yanayi na lumana domin samun nasarar gudanar da ayyukanta.

Ya bayyana jin dadinsa da cewa shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya riga ya fitar da dokar da aka yiwa bita da kuma ka’idojin aiki ga sojoji yayin babban zabe.

Shugaban kasar ya kuma umarci rundunar sojin kasar da su kasance da kwarewa da kuma kiyaye dukkan hakkokin bil’adama yayin gudanar da ayyukansu na tsarin mulki.

Shugaba Buhari ya kuma dora musu alhakin samar da dabaru masu dorewa da za su karfafa kokarinsu wajen tabbatar da tsaron kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: