Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Jigawa ta raba miliyan 37 da dubu 700 ga iyalan wasu ‘yan sanda guda goma da suka rasu

0 101

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Jigawa ta raba cakin kudi na fiye da naira miliyan 37 da dubu 700 ga iyalan wasu ‘yan sanda guda goma da suka rasu a bakin aiki, karkashin shirin asusun tallafawa ‘yan sanda na ofishin babban Sifeton ‘yan sanda na kasa.

A jawabin da ya gabatar bayan raba cakin kudaden ga iyalan marigayan, a madadin babban sifeton ‘yan sanda na kasa, kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Jigawa CP Emmanuel Effiom Ekot ya ce hakan wani kokari ne na tausayawa tare da jinkan iyalan ‘yan sandan ada suka rasu domin inganta rayuwarsu.

Kwamishinan ya kara da cewa rundunar a shirye take ta kula rayuwar iyalan ‘yan sandan da suka rasu lokacin da suke yiwa kasa aiki.

Emmanuel Effiom Ekot daga nan ya bukaci iyalan marigayan su yi cikakken amfani da tallafin kudaden domin kula rayuwarsu.

A jawabinta na godiya a madadin sauran iyalan wadanda suka rasu, Emmanuela Yakubu ta yabawa ofishin babban sifeton ‘yan sanda na kasa da kuma da rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa bisa kulawa da rayuwarsu, inda ta bada tabbacin yin amfani da tallafin domin gudanar da harkokin rayuwarsu ta yau da kullum.

Leave a Reply

%d bloggers like this: