Za a karrama shugaban kasa Buhari da lambar girma mafi daraja a kasar Bissau

0 113

Yau a birnin Bissau na kasar Guinea Bissau za a karrama Shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar girma mafi daraja a kasar, bisa la’akari da gudunmawar da gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da mulkin demokradiyyar a kasar dake yammacin Afrika.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

A cewar Garba Shehu, shugaban kasar zai amsa gayyatar shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoko Embalo, domin bikin na musamman da za a gudanar a fadar shugaban kasar.

Garba Shehu ya sanar da cewa daga cikin abubuwan da Shugaba Buhari zai yi a Bissau sun hada da kaddamar wani titi da aka sanya sunansa a birnin.

Hadimin shugaban kasar ya kara da cewa yayin ziyarar zuwa Bissau, Shugaba Buhari tare da tawagar Najeriya za su shiga tattaunawa diflomasiyya.

Garba Shehu ya sanar da cewa shugaban kasar zai samu rakiyar karamin ministan harkokin waje, Zubairu Dada, da mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Babagana Monguno da daraktan janar na hukumar leken asiri, Ahmed Rufa’i.

Leave a Reply

%d bloggers like this: