Wata gidauniyar zakka da sadaka ta raba dukiyar da ta kai naira triliyan 2.3 cikin shekaru 25

0 88

Gidauniyar zakka da sadaka, wata kungiya a Najeriya ta cika shekaru 25 da kafuwa, yayin bikin cikar shekarun tace iya tsawon lokacin ta raba dukiyar da ta kai naira triliyan 2.3 kai tsaye ga mutane dubu 28, 090.

A wani taron manema labarai data gudanar a Legas, shugaban gidauniyar farfesa Tajuddeen Yusuf, yace tysawon lokacin ta kasance tana ayyukan sadaukarwa domin cigaban al’umma nta hanyar sauya rayuwar jama’a a fadin jihohi 27 a kasar nan.

Yace gidauniyar ta na bayar da tallafi ta fuskoki 15 da suka hada da ayyukan al’umma, rage talauci, tallafawa ilimi da kiwon lafiya, tallafawa kananan yan kasuwa, tallafi ga marayu da zawarawa, ayyuykan tsaftar ruwa da muhalli, samar da abinci da tallafin gaggawa.

Farfesa yace manufar gidauniyar shine rage gibin dake tsakanin mawadata da talakawa.

Babban darakta kuma mamallakin gidauniyar prince Sulaiman Olagunju ya bayyana bikin shekar shekaru 25 din a matsayin wata gagaruwamar nasara mai dorewa da suka cimma

Leave a Reply