Wata kungiya ta bukaci a dakatar da Babandi Isa Gumel, Shugaban Jigawa Savings & Loans Ltd daga shugabancin bankin.

0 432

Ƙungiyar rajin kare gaskiya da ci gaban matasa – Noble Youth Mass Support Association (NYMSA)  ta bukaci Gwamnatin Jihar Jigawa da Babban Bankin Najeriya (CBN) su dauki mataki gaggawa kan zargin cin hanci da almundahana da aka keɓe da Babandi Isa Gumel, Manajan Darakta na Jigawa Savings and Loans Ltd (JSL).

Zargin na da tushe ne daga rahoton da aka shigar kan zargin. Wannan ya sa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Jin Koken Jama’a ta JIhar Jigawa (Jigawa State Public Complaints and Anti-Corruption Commission (JSPCACC)) ta fara bincike har ta gurfanar da shi a gaban kotun Majistare.

Babandi Isa na fuskantar tuhumar, sayar da filaye ba bisa ka’ida ba, cire kudi daga asusun banki ba tare da an yi wani dalili ko ka’ida ba, gaza tura harajin VAT da PAYE zuwa FIRS da JIRS, sayen motar N57m da kudi daga asusun banki, cire N5m zuwa asusun shi na Zenith Bank a ranar 19 ga Janairu 2024, sata da sayar da kadarori a wurare kamar Shuwarin, Kiyawa Road da 744 Housing Estate (Mobile Base), Dutse.

NYMSA ta ce, har yanzu Babandi yana ci gaba da zama a ofis duk da ana shari’a da shi, wannan ya saba da tsarin dokokin da’a a hukumomin kudi da gwamnati. A mafi yawan lokuta, jami’in da ake bincike kan laifin kudi ana dakatar da shi har sai an kammala shari’a, kuma zamansa a ofis na iya kawo cikas ko hana gaskiya fitowa fili.

Sannan yana amfani da matsayinsa domin amfanar da kansa, kamar bai wa ‘yan uwansa kwangiloli da damar da ba su dace ba. Matarsa, wacce ba ma’aikaciya bace ta na tsoma baki cikin harkokin banki. Dan uwansa na daga cikin manyan masu kwangila a cikin bankin.

NYMSA ta bukaci CBN da NDIC su shigo cikin lamarin.

Leave a Reply