‘Yan Bindiga sun kashe mutane 38 bayan karban kudin fansa miliyan ₦50 a jihar Zamfara
Mutanen Kauyen Banga Na Cikin Alhini Bayan Kisan Gilla da ‘Yan Bindiga Suka Yi wa Mutane 38 Duk da An Biya Fansa Naira Miliyan 50
Mutanen kauyen Banga da ke cikin ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun shiga halin damuwa da jimami, bayan da ‘yan bindiga suka kashe mutane 38 da suka yi garkuwa da su, duk da cewa an biya fansa sama da miliyan ₦50.
Shugaban ƙaramar hukumar Kaura-Namoda, Mannir Haidara Kaura, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television. Ya ce, mutane 56 aka sace, sannan daga baya aka saki mutum 18 kacal.
“‘Yan bindiga sun sace mutane 56, amma 18 ne kawai suka dawo,” in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa mutanen da aka sako an kwantar da su a asibiti domin karɓar magani.
Wani mazaunin kauyen mai suna Ibrahim Banga ya shaida wa Channels TV cewa ‘yan bindigar sun shiga kauyen watanni da suka gabata, inda suka sace mutane 53. Sun nemi ₦1 miliyan kan kowane mutum, kuma bayan makonni, al’umma suka haɗa kuɗin suka kai wa masu garkuwar.
Ibrahim ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun saki mutum 18 kacal daga cikin wadanda aka sace.
“Da suka dawo, waɗanda aka sako sun ba da labari cewa ‘yan bindigar sun yanka sauran mutane 35 din ɗaya bayan ɗaya a lokacin da suke tsare da su,” in ji Ibrahim Banga.
Ya roƙi gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara da su ɗauki mataki na gaggawa, ta hanyar tura sojoji zuwa yankin, domin:
- dawo da zaman lafiya,
- ceto sauran da ke hannun ‘yan bindiga,
- da kuma taimakawa wajen dawo da mutanen da suka kaura daga gidajensu.