farfesa Pat Utomi ya ƙaddamar da gwamnatin sa ido mai mambobi daga jam’iyyun adawa, domin sa ido kan ayyukan gwamnatin tarayya Utomi ya ce manufofin gwamnati sun ƙara jefa mutane a talauci, sun ƙarfafa ta’addanci, abin da ya ce ya zama dalilin kafa gwamnatin sa ido Sai dai gwamnati, ta bakin ministan labarai, Mohammed Idris, ta nuna adawa da matakin Utomi, inda ta ce ba mulkin Firaminista ake yi ba.
Masanin tattalin arziki kuma ɗan gwagwarmaya, Farfesa Pat Utomi, ya ƙaddamar da gwamnatin sa ido, wacce ta ƙunshi mambobi daga jam’iyyun adawa daban-daban. Farfesa Pat Utomi ya kaddamar da wannan gwamnatin sa idon a yanar gizo a daren ranar Litinin, inda ya ce za ta rika sa ido kan ayyukan gwamnati tare da ba da shawarwari.