Mutum fiye da miliyan uku ne suka gudanar da aikin Umara a Masallacin Harami a cikin watan Ramadan, a cewar wasu alƙaluma da shafin Haramain Sharifain ya wallafa.

Miliyoyin Musumai ne bisa al’ada ke zuwa masallacin duk watan Ramadan kafin al’amura su sauya sakamakon annobar korona da ta jawo soke yin Hajji da Umara ga ‘yan ƙasar waje a 2020.

Wannan adadi ya nuna irin ci gaban da aka samu wajen sassauta dokokin bayar da tazara.

A watan Maris ne aka bai wa tsofaffi ‘yan shekara 60 damar gudanar da aikin bayan an dakatar da su saboda tsoron kamuwa da cutar.

Cutar korona ta kashe mutum 6,979 a Saudiyya yayin da ƙasar ta yi wa mutum kusan miliyan tara rigakafin cutar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: