Ya kamata sojojin Najeriya su ninka kokarin su domin dakile ta’addanci a Jihar Neja kamar yadda Shugaba Buhari ya basu umarni – Sani Bello

0 67

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya Kuma Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bukaci Sojojin Najeriya su ninka kokarin su domin dakile ta’addanci a Jihar kamar yadda Shugaba Buhari ya basu umarni.

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa biyo bayan karuwar hare-haren ta’addanci a Kananan hukumomin Shiroro da Munya da Rafi da kuma Paikoro na Jihar.

Gwamnan ya bayyana damuwa kan yadda yan bindigar suke cigaba da kaiwa hare-hare a sassan Jihar wanda hakan ne ya sa ake samun asarar rayuwa da Dukiyoyin Al’umma, ciki harda Sojoji.

A cewarsa, karuwar hare-haren yan bindigar a Jihar Neja, na cigaba da dakile kokarin hukumomin tsaro a yankin.

A kwanakin baya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya umarci Sojoji su ninka kokarin su wajen murkushe yan bindigar gaba daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: