Yansanda a jihar Jigawa sun kama wani mai zama shago mai suna Ibrahim Haruna, bisa zargin yiwa wata yarinya yar shekara 6 fyade a yankin karamar hukumar Hadejia.

Mukaddashin kakakin yansanda na jiha, Lawan Adam, a jiya yace Ibrahim Haruna mai shekara 25, mazaunin unguwar Gawuna a nan Hadejia, ya ja yarinyar zuwa shagonsa inda yayi mata fyade.

Yansanda sunce an kama wanda aka zargi a ranar 17 ga watan Yuni biyo bayan korafin da aka samu daga Maryam Kani, mahaifiyar yarinyar da aka yiwa fyaden.

Yansanda sunce an tafi da yarinyar zuwa cibiyar da ake kai wadanda aka yiwa fyade dake Dutse domin duba lafiyarta.

Kakakin na yansanda yace bayan karbar korafi, an gaggauta kama wanda ake zargi inda aka tsare shi domin bincike.

Ya kara da cewa kwamishinan yansanda na jiharnan ya umarci sashen binciken manyan laifuka da ya binciki lamarin domin gurfanar da wanda ake zargi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: